IQNA

Sanar da shirye-shiryen asibitocin Hubbaren Imam Hussain don kula da  Falastinawa suka samu raunuka

15:45 - November 24, 2023
Lambar Labari: 3490198
Karbala (IQNA) Cibiyar Hubbaren Imam Hussain (AS) ta sanar da shirinta na karbar jinyar Falasdinawa da suka jikkata.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ma’aikatar harkokin wajen kasar Iraki ta sanar a hukumance a cikin wata wasika da ta aike wa ofishin jakadancin Falasdinu da ke Bagadaza cewa: Cibiyar Hubbaren Imam Hussain (AS)  a shirye take ta yi wa Falasdinawa da suka jikkata a asibitocin da ke da alaka da su.

An bayyana a cikin wannan wasika cewa: Za a yi aiki tare da kungiyar agaji ta Red Crescent ta Iraki da kuma kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu game da tsarin mika wadanda suka jikkata zuwa asibitocin da ke da alaka da Cibiyar Hubbaren Imam Hussain (AS).

A baya dai Cibiyar Hubbaren Imam Hussain (AS) ta sanar da cewa a shirye take ta karbi wadanda suka jikkata a hare-haren da ‘yan mamaya ke kaiwa mutanen Gaza a asibitocin da ke da alaka da su.

Tun farkon hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ke kai wa zirin Gaza, Palasdinawa 14,854 ne suka yi shahada, wadanda suka hada da yara sama da 6,150 da mata fiye da dubu hudu.

Bugu da kari, kimanin mutane 7,000 ne har yanzu ba a gansu ba ko kuma a karkashin baraguzan ginin. Haka kuma an bar wasu gawarwakin a kan tituna da tituna, baya ga haka, har yanzu ba a san makomar wasu da suka jikkata ba.

 

4183795

 

captcha